12 Agusta 2020 - 09:59
Fiye Da Mutane 80 Ne Su Ka Rasa Rayukansu A Wani Sabon Rikici Da Ya Barke A Kasar Sudan Ta Kudu

Fadan ya barke ne a jita Talata tsakanin sojojin gwamnati da kuma fararen hula masu dauke da makamai a yayin aiwatar da wani shiri na kwance makamai daga hannun wadanda ba sojoji ba.

ABNA24 : Ya zuwa jiyan an tabbatar da mutuwar mutane 81 a fadan da aka yi amfani da manyan bindigogi, kamar yadda kakakin sojan kasar ya sanar.

Kakakin sojan kasar Ruai Koang ya shaidawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa; Matasan da suke dauke da makamai a yankin Greater Tonj ne su ka fara kai farmaki akan sojojin.

Koang ya kara da cewa; Sojoji 55 ne su ka rasa rayukansu sai kuma fararen hula 26.

An sake samun dawowar zaman lafiya a cikin yankin da lamarin ya faru kamar yadda kakakin sojan ya fada.

342/